Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Fasalin Shirin NYSC
Published: June 30, 2026 at 8:30 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Zartarwa a Tarayyar Najeriya (FEC) karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da yin gyare-gyare ga tsarin yi wa kasa hidima (NYSC).

Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Ya ce gyaran zai kunshi cikakken nazari da sake duba tsarin shirin na NYSC domin ya dace da bukatun zamani.

An kafa shirin NYSC a shekarar 1973 bayan yakin basasar Najeriya da nufin karfafa hadin kai da zumunci tsakanin matasa masu digiri daga sassa daban-daban na kasar.

Tsawon shekaru 53 da kafuwar shirin, NYSC ta taimaka wajen hada kan matasa da kuma inganta hadin kan kasa.

Sai dai ministan ya ce sauye-sauyen da suka faru a kasar cikin shekaru da dama sun sa ya zama dole a sake fasalin shirin, yana mai cewa bukatun Najeriya sun canza, kuma ana sa ran manufofin NYSC su ma su dace da sabon yanayin da ake ciki.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: An Bukaci Sabbin Shugabanni Su Yi Jagoranci Nagari da Inganta Ayyukan Jama’a
Next Post: PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen Afrika
Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika
Ga Alamu Jakuna Za Su Bace A Doron Kasa Nan Da Shekaru 5 Labarai
CAF Ta Dakatar Da Kocin Senegal Pape Thiaw Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ƙarin Albashi Zai Fara Aiki Ga Sojojin Najeriya Daga Satumba Afrika
  • CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
  • Wike: Bazamuyi Sake Fubara Ya Sake Samun Nasara Ba Najeriya
  • Amurka Zata Fara Sayar Da Maganin Hana Kiba Da Jin Yunwa Amurka
  • An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
  • Shugaban Amurka Donald Trump Ya Jadda da Kudirinsa Da Kwace Iyakar Greenland Amurka
  • Hukumomin Tsaron Najeriya Ne Suka Bukaci Amurka Ta Turo Musu Sojoji Amurka
  • Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.