Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci masu ruwa da tsaki a kamfanonin ɗab’i na Nijeriya da su rungumi haɗin kai, sasanci da haɗin gwiwa domin bunƙasa masana’antar tare da ƙara mata ƙarfin gogayya a matakin duniya.
Ministan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a wurin Babban Taron Masu Ruwa da Tsaki na Maɗaba’u na Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanar a otal ɗin Nicon Luxury da ke Abuja.
A cewar sa, warware rikicin shugabanci da ya daɗe a Cibiyar Ƙwararrun Maɗaba’u ta Nijeriya (CIPPON) ya samar da wata dama ta sake farfaɗo da masana’antar da kuma amfani da cikakkiyar damar tattalin arzikin ta.
Ya ce: “Tarihi ya ba ku dama ta sake gina wannan masana’anta. Don Allah ku yi amfani da ita, ku yi aiki tare, kuma kowa ya mara wa shugabanci baya domin ku ciyar da wannan sana’a gaba tare.”
Idris ya ce rikicin da ya daɗe yana addabar cibiyar yana daga cikin batutuwan farko da aka gabatar masa bayan ya kama aiki a matsayin minista, inda ya ƙara da cewa ya zaɓi sasanci da tattaunawa ne saboda ya yi imanin cewa hakan ya fi amfani fiye da doguwar shari’a.
Ya bayyana masana’antar ɗab’i a matsayin wata muhimmiyar hanya ta bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi, yana mai cewa idan masu ruwa da tsaki suka kasance tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, masana’antar za ta fi samun goyon bayan gwamnati da manufofin da za su bunƙasa ta.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki tare da CIPPON da sauran hukumomin da abin ya shafa domin ƙarfafa ƙa’idojin ƙwarewa, inganta yanayin gudanar da sana’ar da kuma ƙara gudunmawar masana’antar wajen cigaban ƙasa.
Haka kuma ya buƙaci shugabannin cibiyar da su bai wa kowa dama ba tare da la’akari da saɓanin da ya gabata ba, yana mai cewa shugabanci mai haɗa kowa ne zai samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma kyakkyawan gado ga waɗanda za su zo nan gaba.
Ya kuma shawarci masu sana’ar ɗab’i da su rungumi sababbin fasahohi domin ci gaba da kasancewa masu tasiri a wannan zamani na fasahar dijital.
A nasa jawabin, Shugaban CIPPON kuma Shugaban Majalisar Gudanarwar ta, Koko T. Clement, ya ce cibiyar ta samu cigaba tun bayan rantsar da sabuwar majalisar gudanarwar ta a watan Disamba 2025.
Ya ce sun gudanar da tattaunawa da hukumomin gwamnati domin ƙarfafa ƙa’idojin ƙwarewar sana’a, inganta tsarin tafiyar da masana’antar da kuma samar da manufofin da za su taimaka wajen bunƙasa masana’antar ɗab’i a Nijeriya.
Ya ce: “Duk abin da muke yi domin cigaban wannan cibiya ne, domin amfanin kowane mai bugu, kowane ƙwararren mai aikin marufi, kuma kowane ɗan Nijeriya da ke dogaro da wannan masana’anta. Muna kira ga duk masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare cikin zaman lafiya da fahimtar juna domin abin da ya haɗa mu ya kasance mafi girma fiye da duk wani abin da zai raba mu.”
Taron ya samu halartar shugabannin masana’antar ɗab’i, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Magatakardan CIPPON, Malam Abubakar Ndagi; Babban Jami’in Gudanarwa na KA2 Press Limited, Injiniya Michael Akinola; Daraktan Gudanarwa na kamfanin, Mista Ademola Kasumu da manyan jami’an Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, tare da sauran masu ruwa da tsaki daga masana’antar ɗab’i.


