Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
  • Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya Afrika

Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
Published: July 23, 2026 at 6:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da faɗaɗa tsarin Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya daga rukuni takwas zuwa goma sha biyu, tare da ba da izinin ɗaukar sabbin sojoji dubu 28 domin ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta ƙarfin rundunar wajen fuskantar ƙalubalen tsaro.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce matakin na daga cikin ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na sake fasalin Rundunar Sojin Ƙasa domin ƙara mata inganci wajen gudanar da ayyuka, inganta tsarin jagoranci da umarni, da kuma hanzarta mayar da martani ga barazanar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewar sanarwar, gwamnatin tarayya ta kuma amince da ɗaukar sabbin sojoji dubu 28, tare da ci gaba da samar da manyan kayan aikin soja na zamani, inganta walwalar jami’ai da sojoji, da kuma ƙarfafa shirye-shiryen zamanantar da rundunar.

Sabon tsarin zai sanya Rundunar Sojin Ƙasa ta kasance da rukuni goma sha biyu da za su kasance a muhimman yankuna na ƙasar. Hedikwatar Runduna ta 3 da ke Jos za ta ci gaba da kula da ayyukan soji a jihohin Filato, Bauchi da Gombe.

Haka kuma, za a kafa sabbin hedikwatocin rundunoni a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin City.

Sanarwar ta bayyana cewa aiwatar da wannan sabon tsari za a yi shi kashi biyu. Kashi na farko, wanda ya haɗa da kafa Rundunoni na 5 da na 9 da na 10 tare da sake tsara wasu rundunonin da ake da su, ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen watan Satumban 2026. Kashi na biyu kuma, wanda ya ƙunshi kafa Runduna ta 83 da ƙarin sake fasalin rundunar, ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen watan Disamban shekarar 2026.

Har ila yau, Shugaba Tinubu ya yabawa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Ibrahim Shuaibu, da daukacin jami’ai da dakarun Rundunar Sojin Ƙasa bisa jajircewarsu da ƙwarewarsu wajen kare ikon Najeriya da kuma tabbatar da tsaron ƙasar.

Shugaban ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da zuba jari a harkokin rundunonin tsaro, domin tabbatar da cewa suna da isassun kayan aiki, ƙwararrun ma’aikata da ƙarfin da zai ba su damar kare rayuka, dukiyoyi da martabar ƙasar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa
Next Post: Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hankali Najeriya
Kasar Namibiya Tayi Watsi Da Yarjejeniya Tsakanin Ta Da Kamfanin Total Labarai
Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan Agajin Izalar Jos Sunyi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • Ana Zargin Tsohon Shugaban Kasar Philippines Da Ta’addaci A Lokacin Mulkinsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique Afrika
  • Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya
  • Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
  • ‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Da Mata 13 A Borno Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga Amurka
  • Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.