NPFL SABON KAKAR LIG TA 2026/27 ZA TA FARA RANA JUMA’A
Za a fara kakar gasar Firimiya ta Najeriya, NPFL, ta 2026/27 a yau Juma’a, 28 ga watan Agusta, inda Shooting Stars za ta karɓi bakuncin sabuwar ƙungiyar Inter Lagos a filin wasa na Lekan Salami da ke Ibadan da ƙarfe 4:00 na yamma.
Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta kuma tabbatar da jami’an da za su jagoranci wasannin makon farko na gasar.
Wasan da zai buɗe kakar gasar zai kasance tsakanin Shooting Stars, wadda ta lashe kofin NPFL sau biyar, da Inter Lagos, wadda ta samu damar shiga gasar NPFL a karon farko bayan samun ɗaukaka zuwa matakin farko.
Kwamitin Raya Alƙalan Wasan NFF ya naɗa Bashir Salisu a matsayin babban alƙalin wasan, yayin da Ahmed M. Tijani da Muud Zango za su kasance mataimakansa. Gata Muhd L. kuma shi ne jami’in wasa na huɗu.
Sauran wasannin makon farko guda tara za a buga su ne ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta, duk da ƙarfe 4:00 na yamma.
Daga cikin manyan wasannin akwai Rangers da za ta fara kare kambunta a gida yayin da za ta karɓi Katsina United. Rivers United kuma za ta karɓi Plateau United, yayin da Kwara United za ta fafata da Kano Pillars.
Niger Tornadoes za ta karɓi Enyimba a Minna, yayin da Doma United za ta kara da Sporting Lagos.
Haka kuma, Ikorodu City za ta karɓi Ranchers Bees, Abia Warriors za ta kara da Kun Khalifat, Barau FC za ta fafata da Nasarawa United, yayin da Bendel Insurance za ta karɓi Warri Wolves.
Wasan farko tsakanin Shooting Stars da Inter Lagos na da muhimmanci musamman, saboda Shooting Stars za ta fara sabon kakar gasar ƙarƙashin jagorancin koci Salisu Yusuf, yayin da Inter Lagos za ta buga gasar NPFL a karon farko a tarihinta.
Ƙungiyoyin biyu sun taɓa fuskantar juna a wasan sada zumunta na share fagen kakar wasa a ranar 4 ga Agusta, inda suka tashi kunnen doki 0-0.
### Wasannin Makon Farko
**Juma’a, 28 ga Agusta**
Shooting Stars vs Inter Lagos — 4:00 na yamma
**Lahadi, 30 ga Agusta**
Ikorodu City vs Ranchers Bees — 4:00 na yamma
Abia Warriors vs Kun Khalifat — 4:00 na yamma
Barau FC vs Nasarawa United — 4:00 na yamma
Bendel Insurance vs Warri Wolves — 4:00 na yamma
Rangers vs Katsina United — 4:00 na yamma
Rivers United vs Plateau United — 4:00 na yamma
Kwara United vs Kano Pillars — 4:00 na yamma
Niger Tornadoes vs Enyimba — 4:00 na yamma
Doma United vs Sporting Lagos — 4:00 na yamma
Hankali yanzu ya koma Ibadan, inda Shooting Stars da Inter Lagos za su buɗe kakar gasar NPFL ta 2026/27 a hukumance ranar Juma’a.


