Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amupitan Ya Gargadi Jami’an INEC Kan Cin Hanci Afrika
  • Keke NAPEP Ta Kashe Yara Biyar, Wasu Uku Rai Kwakwai Afrika
  • Ƙungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Masussuka Afrika
  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro Afrika
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN Afrika

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Yahaya Masussuka A Dutsin-Ma
Published: October 27, 2026 at 6:01 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: October 27, 2026

Rundunar ’Yan Sandan jihar Katsina a Najeriya ta tabbatar da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar, sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai musu.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 7:30 na dare, a gaban gidan malamin da ke Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina, inda wasu mutum biyu dauke da makamai, waɗanda suke kan babur, suka buɗe musu wuta, har suka yi musu raunukan da suka yi sanadin mutuwarsu.

Bayan samun rahoton faruwar lamarin, Jami’in ’Yan Sandan da ke kula da sashen Dutsin-Ma (DPO) ya jagoranci tawagar jami’an rundunar zuwa wurin da lamarin ya faru.

Nan take aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa domin ba su kulawar likitoci, amma abin takaici, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da cewa sun rasu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage ya bayar da umarnin tura jami’an dabarun yaƙi da aikata laifuka da sauran jami’an tsaro zuwa yankin.

Rundunar ta ce an fara gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda ake zargi da aikata kisan da suka tsere, domin cafke su da gurfanar da su a gaban shari’a.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, abokansu da mabiyansu, da kuma al’ummar Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma baki ɗaya bisa wannan babban rashi.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta cafke waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da an yi musu hukunci bisa doka.

Rundunar ta ƙara da cewa za ta sanar da jama’a duk wani sabon bayani da aka samu dangane da lamarin a nan gaba.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro
Next Post: Ƙungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Masussuka

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Bauchi: Ba Zamu Bude Makarantu Ba Sai 2026 Labarai
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru Afrika
Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Amupitan Ya Gargadi Jami’an INEC Kan Cin Hanci
  • Keke NAPEP Ta Kashe Yara Biyar, Wasu Uku Rai Kwakwai
  • Ƙungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Masussuka
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Yahaya Masussuka A Dutsin-Ma
  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Gano Wasu Boma Bomai Da Aka Binne A Jihar Neja Najeriya
  • Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
  • Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka Afrika
  • Prime Ministan Senegal Ya Bayyana Shirin Sauya Sheka Afrika
  • Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran Amurka
  • Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.