Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amupitan Ya Gargadi Jami’an INEC Kan Cin Hanci Afrika
  • Keke NAPEP Ta Kashe Yara Biyar, Wasu Uku Rai Kwakwai Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Yahaya Masussuka A Dutsin-Ma Labarai
  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro Afrika
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN Afrika

Ƙungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Masussuka
Published: October 27, 2026 at 12:37 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar Ansaru, mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, ta ɗauki alhakin kashe Mallam Yahaya Masussuka, inda ta zarge shi da kasancewa kafiri.

Wani lauya Audu Bulama Bukarti a shafinsa na Facebook ga wallafa cewa, Ƙungiyar ta tabbatar da ɗaukar alhakin kisan ne a wani saƙon murya da ta fitar a yau talata.

A cikin saƙon, Ansaru ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare. Mai magana a cikin saƙon ya ambaci cewa harin ya faru ne ranar Talata, amma hakan na iya zama kuskure, domin lamarin ya faru ne ranar Litinin.

Ansaru ta zargi Sheikh Yahaya Masussuka da adawa da Musulunci, amma ba ta bayyana wani takamaiman laifi da ya aikata ba. Sai dai, saƙon ya nuna cewa matsayinsa na ƙarfafa tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban da kuma zaman lafiya na iya kasancewa cikin abubuwan da suka jawo harin.

Ansaru ta balle daga ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2012 sakamakon rashin jituwa da shugabancin Abubakar Shekau. Tun daga lokacin, ƙungiyar ta gudanar da ayyukanta musamman a Arewa maso Yamma, ciki har da jihohin Zamfara, Kaduna da Neja.

Ba abin mamaki ba ne a ce Ansaru da hannu a wannan hari, duba da cewa Malam Masussuka na shirin gudanar da wani babban taron zaman lafiya.

Wannan na iya zama ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ya zama abin hari, ganin yadda ƙungiyar ke adawa da zaman lafiya da zaman tare tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Yahaya Masussuka A Dutsin-Ma
Next Post: Keke NAPEP Ta Kashe Yara Biyar, Wasu Uku Rai Kwakwai

Karin Labarai Masu Alaka

Manoma Da Makiyaya: An Bukaci A Gaggauta Tantance Hanyoyin Shanu Da Iyakoki A Dukku Afrika
Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
ECOWAS Ta Saka Dokar Ta Baci A Afrika Ta Yamma Afrika
Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

https://www.youtube.com/watch?v=sainfSmn-EQ

Sabbin Labarai

  • Amupitan Ya Gargadi Jami’an INEC Kan Cin Hanci
  • Keke NAPEP Ta Kashe Yara Biyar, Wasu Uku Rai Kwakwai
  • Ƙungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Masussuka
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Yahaya Masussuka A Dutsin-Ma
  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Pakistan Zata Karbi Tattaunawar Rikicin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Ganduje Ne Yasa Aka Kama Ni Inji Muhuyi Magaji Najeriya
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
  • Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai
  • Rundunar Operation Endurance Peace Ta Gano Wajen Kera Makamai A Jihar Filato Afrika
  • Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.