Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Musulmi a faɗin Najeriya da su rungumi koyarwa da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW), yayin da suke bikin Maulidin Annabi na shekarar 2026.
Shugaban ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata.
Ya ce bikin Maulidi bai kamata ya tsaya kawai kan tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) ba, sai dai ya kasance wata dama ga Musulmi su yi nazari, addu’a tare da koyon darussa daga kyakkyawar rayuwar Annabin.
Shugaba Tinubu ya buƙaci Musulmi su riƙe koyarwar Annabin, musamman ibada, haƙuri, juriya, yafiya, tawali’u da sadaukar da kai ga taimakon al’umma.
Ya kuma yi kira ga malaman addini da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa Najeriya addu’a tare da jan hankalin mabiyansu su aiwatar da darussan da suka koya daga rayuwar Annabi Muhammad (SAW) wajen ƙara kishin ƙasa.
Haka kuma, Shugaban ya buƙaci Musulmin da ke bikin Maulidi su tallafa wa mabukata da masu rauni, tare da nuna musu ƙauna da kulawa.
Shugaba Tinubu ya kuma yi kira da a ci gaba da yi wa ƙasar addu’a domin samun nasara a kan matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar wasu sassan Najeriya.


