Cibiyar Sasanta Addinai ta Interfaith Mediation Centre (IMC) da ke Kaduna, ta yi kira ga al’ummar Najeriya da su yi amfani da damar bikin Maulidin Annabi na shekarar 2026 wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai, mutunta juna da kyakkyawar fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban a faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Cibiyar, Mista Samson Auta, ya fitar ga manema labarai, IMC ta taya al’ummar Musulmi murnar wannan muhimmiyar rana, tare da bayyana Maulidin a matsayin lokaci na yin tunani a kan rayuwar Annabi Muhammad (SAW) da kuma sabunta ƙudurin gina al’umma mai cike da zaman lafiya da jituwa.
Cibiyar ta ce sama da shekaru 30 tana jagorantar ƙoƙarin haɗa kan al’ummomin mabiya addinai daban-daban ta hanyar tattaunawa, sulhu, sasanci da kuma hanyoyin warware rikice-rikice ba tare da amfani da tashin hankali ba.
A cewar IMC, rayuwa da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW) sun kasance tushen jagoranci da koyi ga bil’adama, musamman wajen nuna tausayi, haƙuri, adalci, daidaito da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Cibiyar ta jaddada cewa bambancin al’adu, ƙabilu da addinai da ke akwai a Najeriya ya kamata ya zama ƙarfin ƙasar, ba abin da zai haddasa rarrabuwar kai ba.
Ta yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi mutunta juna, fahimtar juna, haƙuri da zaman lafiya, tare da guje wa duk wani abu da zai iya haifar da rikici ko ƙiyayya.
IMC ta kuma buƙaci ’yan ƙasa, shugabannin addinai da siyasa, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki da su yi nazari mai zurfi kan koyarwar Alƙur’ani, musamman dangane da yadda ya kamata mutane su mu’amalanci makwabtansu da kuma gina kyakkyawar dangantaka tsakanin al’ummomi.
Cibiyar ta yi kira da a yi watsi da nuna wariya, kalaman ƙiyayya, rashin haƙuri da tashin hankali, tare da ƙarfafa adalci a cikin al’umma, kare masu rauni, da kuma tallafa wa hanyoyin sulhu da tattaunawa cikin lumana.
IMC ta ambato ayar Alƙur’ani ta 49:13 da ke tunatar da bil’adama cewa Allah Ya halicci mutane daga namiji da mace, Ya kuma sanya su al’ummai da ƙabilu domin su san juna, tana mai cewa wannan koyarwa na ƙarfafa girmama bambance-bambancen da ke tsakanin al’umma.
Haka kuma, ta ambato ayar Alƙur’ani ta 41:34 da ke koyar da cewa a mayar da mugunta da abin da ya fi kyau, tana mai cewa irin wannan hali na iya sauya ƙiyayya zuwa abota.
Cibiyar ta bukaci al’umma da kada su tsaya kan shagulgulan Maulidi kawai, sai dai su mayar da kyawawan ɗabi’u da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) zuwa aikace a rayuwarsu ta yau da kullum.
IMC ta bayyana fatan cewa darussan da ake samu daga Maulidin za su taimaka wajen ƙara haɗin kai, tausayi, adalci da zaman lafiya a Kaduna, Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Cibiyar ta kuma taya al’ummar Musulmi murnar Maulidin Annabi Muhammad (SAW), tare da addu’ar Allah Ya tabbatar da zaman lafiya da jituwa a faɗin Najeriya.
Barka da Maulidi!


