Wani Dan kasuwa kuma mai tallafa wa al’umma, Ahmed Shuaibu Gara Gombe, ya sanar da dakatar da ayyukan tallafa wa al’umma da yake gudanarwa a faɗin Jihar Gombe, bisa zargin fuskantar cin zarafin siyasa da kuma tsoratarwa.
Ayyukan da dakatarwar ta shafa sun haɗa da gasar ƙwallon ƙafa ta Emir’s Championship Cup, wadda ta kai matakin wasan kusa da na ƙarshe, da kuma shirye-shiryen bikin cika shekaru 100 da kafuwar Hassan Central Primary School da ke Gombe.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Azubuike Nathaniel, ya sanya wa hannu, Gara Gombe ya bayyana cewa shirye-shiryen da ake gudanarwa ƙarƙashin ƙungiyoyin Green with Green da Gombe Grassroot Movement sun taka muhimmiyar rawa wajen gano tare da bunƙasa baiwar matasa, ƙarfafa haɗin kai da kuma inganta zaman lafiya a jihar.
Sai dai ya yi zargin cewa dakatar da ayyukan ta biyo bayan wani shiri na cin zarafinsa ta fuskar siyasa, inda ya yi zargin cewa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, da wasu makusantansa na da hannu a lamarin.
Gara Gombe ya kuma yi zargin cewa ana amfani da wasu jami’an shari’a da na ’yan sanda wajen tsoratar da shi da kuma muzanta shi. Ya danganta abin da ke faruwa da goyon bayan da ya bayyana wa Farfesa Isa Ali Pantami da kuma Aminu Yuguda.
Ya ce ya kai ƙorafinsa gaban kotuna, ofishin Sufeto-Janar na ’yan sanda da kuma Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda, domin neman ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.
A cewarsa, dakatar da ayyukan za ta ci gaba da kasancewa har sai an fitar da wata sanarwa ta gaba, yayin da yake mai da hankali wajen kare haƙƙoƙinsa da neman mafita ta hanyar doka.
Gara Gombe bai bayyana lokacin da za a iya dawo da ayyukan ba, yayin da dakatarwar ke shafar shirye-shiryen da suka haɗa da gasar ƙwallon ƙafa da kuma bikin cika shekaru 100 na makarantar.
Ya zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, ba a samu martanin da aka tabbatar daga gwamnatin Jihar Gombe kan zarge-zargen da Gara Gombe ya gabatar ba.


