Shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky, ya fada ranar litinin cewa, shawarwari da aka gudanar da jami’an Amurka da turai, da zummar kawo karshen yakin kasar da Rasha da yanzu ya kusa cika shekaru hudu, akwai alamar zai haifar da da mai ido.
Wakilan Ukraine karkashin jagorancin wani babban jami’in kasar Rustem Umerov, tare da wakilai daga turai sun gudanar da shawarwari da jakadun Amurka na musamman ciki har da wadanda aka yi a baya bayan nan a Florida.
Haka nan shi ma wakilin Rasha Kirill Dmitriev, wanda jakadan shugaba Putin kan zuba jari, shima ya gudanar da shawarwari da jami’an Amurka a zaman da suka yi a jihar Florida.
Wakilan duka sassan biyu, sun fada ranar Litinin cewa za su koma gida domin sanar kasashen na su kan abubuwa da suka tattauna akai.
A bangaren Amurka kuma jakadan shugaba Trump Steve Witkoff, da surkin Trump Jared Kushner ne suka wakilci Washington.
A jawabin da ya sabawa yi wa al’ummar kasarsa a ko wani dare, shugaba Zelensky yace akwai bukatar a tsananta matsin lamba kan Rasha domin rage mata kwarin guiwar kaddamar da yake yake.


