Wassu ‘yan mata da aka ci zarafinsu ta hanyar yin musu fyade, sun karfafawa gwiwan sauran mata da dukkan wadanda ke fuskantar kuntatawa, su rika fitowa karara suna bayyana matsalarsu ga hukumomi da suak dace, don samun adalci.
A ci gaba da yakin neman kawar da duk wani nau’i na cin zarafi, musamman ma ga mata, a kwanaki goma sha shida da majalisar dinkin duniya ta kebe, kungiyar ‘yan jarida mata, reshen jahar Filato ta gabatar da wassu ‘yan mata biyu ga asibitin kwararru na jahar, don ci gaba da duba lafiyarsu.
Chidimma Augustine wacce aka yi wa fyade, ta kuma sami ciki, da yanzu haka ke wata biyar, tace wanda ya mata fyaden ya ki amincewa, balle ma ya dauki nauyin kaita awu, wanda ya cewarta yace yana bin mahaifinta bashin naira dubu biyar.

Ita ma Justina Dusu wanda tace saurayin ta ne ya mata ciki, bayan ta bayyana masa halin da take ciki, ya rufa tad a bugu da sara da adda har ya fasa mata kwayar ido.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida mata, reshen jahar Filato, Madam Grace Akwe Gotip tace kungiyar na bukatar hadin kan al’umma wajen hana cin zarafin mata da taimaka wa wadanda suka fuskanci cin zarafi.

Shima shugaban wata kungiyar matasa dake yaki da cin zarafin al’umma, YIAHVA, Mr Pwakim Jacob Choji, yace tilas sai hukumomi sun aiwatar da dokoki masu tsauri, don kau da cin zarafin al’umma.
Dakta Sa’idu Barnabas, wanda ya karbi ‘yan matan a madadin shugaban asibitin, yace za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ‘yan matan sun sami kulawa mai nagarta.


