Shugabanni daga sassa dabam-dabam na duniya sun yi alkawarin samar da kudi Dala miliyan dubu daya da dari tara, domin karfafa yunkurin kare yara miliyan 370 daga cutar shan inna, ko Polio.
Wannan alkawari da aka yi jiya litinin yana zuwa ne a daidai lokacin da manyan masu bada agaji suke tsuke bakin aljihu.
Duk da wannan alkawarin, ana sa ran kasafin kudi na Shirin Kawar da Cutar Polio a Duniya, wanda kawance ne na Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya da Gidauniyar Gates, zai ragu da kashi 30 cikin 100 a shekarar da zamu shiga, kuma zai fuskanci gibi har na dala miliyan dubu daya da dari bakwai daga nan zuwa shekarar 2029.
A dalilin haka ne hukumomi da kungiyoyin dake cikin wannan kawancen Shirin Kawar da Cutar Polio din suka ce zasu mayar da hankali wajen bincike da bin sawu tare da yin rigakafi a yankunan da aka fi fuskantar kasadar yaduwar cutar.
Darekta janar na hukumar kiwon lafiya ta Duniya, Tedros Ghebreyesus, yace wannan alkawarin tallafin da aka yi jiya a Abu Dhabi zai zamo ginshiki wajen taimakawa shirin kaiwa ga yara a kasashen da har yanzu akwai wannan cuta ta Polio domin hana yaduwarta a duniya.
Kungiyoyi da hukumomi da ma kasashe da dama sun yi alkawarin bada tallafi a wajen taron na jiya, cikinsu har da Gidauniyar Gates wadda ta ce zata bada Dala miliyan dubu daya da dari biyu, sai kuma kungiyar Rotary International wadda ta yi alkawarin Dala miliyan 450.


