Kasar Morocco ta fara rarraba kayayyakin agaji a fadin kasar domin taimakawa dubban ‘yan kasar dake fuskantar tsananin sanyin hunturu da ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da dusar kankara mai yawa a sassan dake kan tuddai da tsaunuka.
Ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ta kashe mutane 37 ranar klahadi a lardin Safi dake bakin gabar teku a kasar, ta lalata gidaje da shaguna 70 ta kuma tafi da motoci tare da rushe hanyoyi.
Za a rarraba wadannan kayayyakin agaji da suka hada da abinci da barguna ne a larduna 28 da suke fama da tsananin sanyi hunturu da dusar kankara, sannan hukumomi suka ce gidaje kimanin dubu 73 za a rarraba ma wadannan kayayyaki.
Ranar talata, hukumomi sun fitar da kashedin fuskantar dusar kankarar da yawanta zai kai centimita 80, watau inci 31 a kwance a kasa a yankunan da suke kan tuddan tsaunukan Atlas, yayin da akasarn yankunan tsakiya da arewacin kasar zasu fuskanci ambaliya a saboda ruwan sama da ake sa ran zai kai milimita 50.
A yanzu haka ma, dusar kankarar da ta zuba a tsaunukan Ouarzazate mai tazarar kilomita 500 a kudu maso gabas da rabat babban birnin kasar, ta kai santimita 50, kuma tsananin sanyi ya kai da komai aka ajiye a waje zai daskare ya koma kankara


