‘Yan raji da jigogin hamayya na kasar Tunisiya sun fantsama kan titunan kasar ranar asabar suna zanga-zangar hadin guiwa da ba a saba ganin irinta ba, ta adawa da shugaba Kais Saied, suna bukatar da a kawo karshen mulkin mutum guda da maido da dimokuradiyya a kasar.
Zanga-zangar dai ta biyo bayan wadda aka shafe makonni uku ana yi, kuma ta nuna airin karin hadin kan da ake samu a tsakanin kungiyoyin hamayya da na al’umma wajen adawa da matakan da ba a taba gani ba a kasar na murkushe masu sukar lamirin shugaban.
Daruruwan mutane sun yi sun hadu a babban birnin kasar dauke da hotunan ‘yan hamayya, da ‘yan jarida da ‘yan raji da aka kama aka kulle.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce Saied ya kawar da ‘yancin walwala a kasar Tunisiya, ya maida kasar baki dayanta tamkar kurkuku, tun lokacin da ya ba ma kansa ikon gudanar da komai ta hanyar yin mulki bisa umurninsa shi kadai a shekarar 2021.


