Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai shiga jam’iyya mai mulki ta APC a hukumance a ranar Litinin, kamar yadda Wata Majiya ta rawaito.
Abba Yusuf, wanda shi kaɗai ne gwamna a jam’iyyar NNPP, ya riga ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen sauya shekar tasa.
Majiyoyi da ke da masaniya kan shirin sauya shekar gwamnan sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe, ne za su karɓi gwamnan a Abuja.
Tuni dai an dawo da jagoran APC a Kano, Abdullahi Ganduje, daga wata tafiya da yake yi a Dubai, haka kuma an umarci shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da ya taƙaita ziyarar sa ta Umara domin ya miƙa katin zama ɗan APC ga gwamnan a mazabarsa ta Diso, da ke Karamar Hukumar Gwale a jihar Kano, a cikin makon nan.


