Allah ya yi wa Sarkin Hausawan Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Ali Ɗahiru Zungeru bayan shafe shekaru huɗu bisa wannan karaga wadda ya gada daga babban wansa.
Sarkin wanda ya rasu da yammacin ranar Litinin, za’ayi mishi sutura yau Talata da misalin ƙarfe 10 na safe tare da binne shi a cikin gidansa da ke Unguwar Sabo a Ibadan, kamar yadda aka yi wa iyayensa da kakanninsa da ya yi gadon sarautar daga garesu.


