Babban kamfanin dake auna tattalin arzikin kasashe da kamfanoni da ake kira S&P, yace kasashen Afirka suna fuskantar kasada sosai saboda tulin bashi da suke kan su, yayinda jadawalin biyan basussuka a bana yake karatowa, wadda ke kara matsin lamba kan kasashen.
A cikin rahoton da kamfanin yake wallafawa a duk shekara, da yake duba makomar tattalin arzikin kasashe dake nahiyar, da ya wallafa a ranar Litinin, yace yawan bashin da kasashen za su biya a bana, ya fi abunda ke kan su a shekara ta 2012.
Kamfanin na S&P yace yawan bashi da karancin samun kudadaden shiga zai ci gaba da barazana yayinda kudaden da ake sa ran kasashen za su biya a bana ya haura dala bilyan 90.
Kasar Masar ko Egypt itace kan gaba da kashi daya cikin uku na wannan adadi wato bilyan 27 na uwar kudi da zata biya, biye da ita sai Angola, da Afirka ta kudu, da kuma Najeriya.


