Burkina Faso ta tsare sojojin Najeriya 11, ta kuma kwace jirgin saman NAF saboda shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin sojin Burkina Fason ce, ta tabbatar da tsare jami’an sojan Najeriya 11 tare da kwace wani jirgin dakon kaya na rundunar sojin saman Najeriya (NAF) bayan ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba sannan ya yi saukar gaggawa.
A cikin sanarwar da Kungiyar Kasashen Sahel (Alliance of Sahel States – AES) ta fitar a daren Litinin, an ce jirgin C-130 na sojin saman Najeriya ya yi saukar gaggawa a Bobo Dioulasso a ranar 8 ga Disamba, 2025, sakamakon matsalar fasaha yayin da yake shawagi a cikin sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izinin shiga ba.
AES dai ƙungiya ce da ta ƙunshi Burkina Faso, Nijar da Mali, dukkaninsu kuma suna ƙarƙashin mulkin soja.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa jirgin na ɗauke da matuka biyu da kuma fasinjoji tara dukkansu jami’an sojan Najeriya ne, ana tsare da su a halin yanzu a hannun hukumomin Burkina Faso.
Kungiyar AES ta yi Allah wadai da lamarin, tana mai cewa hakan babban take hakkin kasa da tauye ikon mallakar sararin samaniya ne amma kuma an kaddamar da cikakken bincike domin gano hakikanin dalilin shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
A martaninsu, AES ta sanar da cewa dakarun kasashen uku sun shiga matakin tsaro mafi girma ne, haka kuma, an bai wa rundunonin tsaro izinin amfani da makaman kare sararin samaniya da na harbo jiragen da zasu karya dokokin sararin samaniyar su.


