Daruruwan mutane sun yi macin yau jumma’a a titunan babban birnin Guinea-Bissau, domin nuna rashin jin dadinsu da juyin mulkin da aka yi a watan da ya shige, tare da neman a sako shugabannin hamayya da aka kama aka tsare.
Masu zanga zanga sun yi arangama da dakarun tsaro a Bissau a yayin da suka toshe hanyoyi ta hanyar kona tayu da kuma yin kiran da a sako Domingos Pereira, shugaban jam’iyyar hamayya wanda aka kama a lokacin juyin mulkin.
Hafsoshin soja sun hambarar da shugaba Umaero Sissoco Embalo a ranar 26 ga watan nuwamba, kwana daya kafin hukumar zabe ta kasar ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi.
Sojojin sun nada manjo janar Horta Inta-a a matsayin shugaban kasar na wucin gadi.
A yayin da wannan ke faruwa ne kuma shugabannin kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yankin na Afirka ta yamma, ECOWAS, suke shirin ganawa a Abuja, babban birnin tarayyar Naeriya domin tattauna lamarin na kasar Ginea-Bissau, tare da nazarin kafa mata takunkumi.


