Hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Faransa ta bukaci jiragen sama ranar Litinin da su soke kashi 15 cikin dari na jiragen da zasu tashi daga filayen jiragen sama na Orly da Charles De Gaulle, har zuwa can da daddare, bayan da dusar kankara me yawan gaske ta sauka a Paris, babban birnin kasar.
Wani me magana da yawun hukumar ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa kamfanonin jiragen suna da damar su zabi wadanne jirage zasu soke, abin da ake so de su rage jiragen da zasu tashi da sauka.


