Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ayyana dokar ta ɓaci a yankin.
Shugaban ƙungiyar ta ECOWAS, Omar Touray, ne ya sanar da hakan a ranar Talata, yayin zaman taron majalisar tsaro na 55, na matakin ministoci a Abuja.
An kira taron ne saboda jerin juyin mulki da yunkurin tayar da hankula da aka samu a ƙasashen yankin kwanan nan.


