Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Farashin Danyen Mai Da Iskar Gas Ya Tashi
Published: March 4, 2026 at 8:23 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Farashin danyen mai da iskar gas sunyi tashin gowron zabbi a ranar talata, saboda harin da Amurka da Isra’ila suke kaiwa kan Iran, ya tsaida jigilar makamashi daga gabas ta tsakiya, Iran tana kai hari kan jiragen ruwa da tashoshin makamashi, da rufe hanyoyin zirga zirgar ruwa a yankin Gulf, kuma hakan ya tilasta tsaida ayyukan mai da iskar gas a daga Qatar zuwa Iraqi.

Danyen mai da ake kira Brent ya tashi da kashi takwas cikin dari a yau talata-sama da dala 83 akan ko wani gangan mai daya, farashi mafi yawa rabon ayi cinikinsa kan haka tun cikin watan yulin shekara ta 2024, wanda ya nuna farashin ya karu da fiye da kashi 15 tun ranar Jumma’a. Farashin iskar gas a turai ya tashi da kamar kashi 40 cikin dari, kamin daga baya ya sauka, wanda kari ne kan tashin farashin zuwa kashi 40 cikin dari a ranar litinin. Ha kama farashin sukari, da taki duk sun tashi.

Yakin yana iya janyo sabon hauhawar farashin kayayyaki wadda zai iya tsaida farfadowar tattalin arziki a turai da asiya, musamman idan artabun da ake yi ya dauki lokaci mai tsawo, a yankin da yake samar da kusan kashi daya cikin uku na makamashi da duniya take amfani da shi.

Afrika, Kimiya, Labarai

Post navigation

Previous Post: Jam’iyyar APC Ta Rantsar Da Sabbin Shugabanni a Jihar Neja
Next Post: Kamfanin Magani Na Aspen Yayi Gagarumar Asara A Cinikayya

Karin Labarai Masu Alaka

Fafaroma Leo Zai Ziyarci Kasashen Afirka Amurka
Kasar Aljeriya Ta Soke Yarjejeniyar Jirgin Sama Tsakaninta Da Daular Larabawa Labarai
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
Fiye Da Mutane 200 Sun Rasa Rayukansu A Wajen Hakar Ma’adanai Labarai
Akalla Mutane 8 Sun Mutu Biyo Bayan Bindiga Da Wata Tanka Tayi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sama Da Zawiyya 100 Ne Suka Samu Tallafin Kayan Abinci Daga Al’mustapha Haji Sufi
  • Wata Kotu A Abuja Ta Wanke Abba Kyari
  • Ko Arsenal Zata Iya Lashe Gasar Firimiya lig Na Bana
  • Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage
  • Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Da Haɗin Guiwar Gwamnatin Jihar Zamfara Suna Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihar Rumbun Hotuna
  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai
  • Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida Afrika
  • Hukumar ICPC Ta Kwato Makudan Kudade Rediyo
  • Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
  • Menene Illar Yada Labaran Karya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani Labarai
  • Soyinka Ya soki Yawan Jami’an Tsaron Da Ake Bai Wa Seyi Tinubu Najeriya
  • Jami’an Tsaron Pakistan Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.