Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Zama Abin Alfahari Ga Najeriya Bayan Lashe Gasar Alƙur’ani Ta Duniya Afrika
  • INEC Ta Ce Ta Kammala Shirye-Shiryen Zaɓen Cike Gurbi A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini Afrika
  • Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji Afrika
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika

Gabanin Zaɓe: Jam’iyyun Siyasa Sun Ƙuduri Aniyar Kare Zaman Lafiyar Jihar Gombe
Published: September 15, 2026 at 7:10 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su guji tashin hankali, daba, kalaman ƙiyayya da duk wani nau’in rashin da’a a harkokin zaɓe, gabanin zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai na ranar 19 ga Satumba da kuma Babban Zaɓen 2027.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, mnips, fwc, psc(+), ya yi wannan kiran ne a lokacin wani taron haɗin gwiwa na tsaro da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin hukumomin tsaro da jam’iyyun siyasa a jihar.

Kwamishinan ya ce taron wata dama ce ta sake jaddada aniyar dukkan masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da gudanar da zaɓuka cikin lumana, gaskiya da adalci a Jihar Gombe.

Ya ce duk da cewa fafatawar siyasa muhimmin ɓangare ne na dimokuraɗiyya, dole ne a gudanar da ita cikin bin doka, mutunta juna da kuma ɗabi’ar siyasa mai nagarta.

CP Chuso ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ƙara amfani da kafafen sada zumunta wajen aikata abin da ya kira “dijital daba”, ta hanyar yin barazana ga abokan hamayya, yaɗa saƙonnin tayar da hankali, ƙirƙira da yaɗa labaran ƙarya da kuma tunzura jama’a.

Ya buƙaci ’yan siyasa da magoya bayansu da su yi taka-tsantsan wajen amfani da kafafen sada zumunta, tare da tabbatar da sahihancin bayanan da suke yaɗawa kafin su rarraba su.

Kwamishinan ya kuma buƙaci jam’iyyun siyasa da ’yan takara su wayar da kan magoya bayansu, musamman matasa, tare da hana amfani da su wajen aikata tashin hankali.

Ya ce babu wata manufa ta siyasa da ta kai darajar rayuwar mutum, ’yancinsa ko makomarsa.

CP Chuso ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro a Jihar Gombe za su ci gaba da samar da ingantaccen yanayi da zai ba jama’a damar gudanar da ayyukansu na dimokuraɗiyya cikin kwanciyar hankali.

Ya ce rundunar za ta kasance mai ƙwarewa, rashin son kai da kuma tsayin daka wajen tabbatar da bin doka, tare da ɗaukar matakin da ya dace kan duk wanda ya yi ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiyar jihar.

Kwamishinan ya kuma shawarci ’yan siyasa da su yi amfani da hanyoyin doka da kundin tsarin mulki wajen warware duk wata takaddama da za ta taso, maimakon komawa ga tashin hankali ko ɗaukar doka a hannu.

A nasu ɓangaren, wakilan jam’iyyun siyasa da suka haɗa da APC, PDP, ADC da Labour Party, da Sani Abubakar Dadawagga Shugaban na Jam’iyar SDP sauran jam’iyyu, sun yaba wa Kwamishinan ’Yan Sandan bisa shirya taron.

Sun ce irin wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da yanayin siyasa mai cike da zaman lafiya a jihar, tare da ba da tabbacin cewa za su gudanar da harkokinsu bisa doka da ƙa’idojin da hukumomin zaɓe suka gindaya.

Wakilan jam’iyyun sun kuma tabbatar da aniyarsu ta bin doka da oda, tare da gudanar da yakin neman zaɓe da sauran harkokin siyasa cikin lumana.

Shi ma wakilin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, a Jihar Gombe, Alhaji Aliko Muhammad, ya tabbatar da shirye-shiryen hukumar na gudanar da zaɓuka cikin ’yanci, adalci da sahihanci.

Ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da ’yan takara da su kiyaye doka da oda, tare da bin ƙa’idojin da hukumar ta tanada a duk tsawon lokacin gudanar da harkokin zaɓe.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana yarjejeniyar zaman lafiyar a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da cewa zaɓen cike gurbin ranar 19 ga Satumba da kuma Babban Zaɓen 2027 sun gudana cikin kwanciyar hankali.

Sun kuma jaddada cewa kare zaman lafiyar Jihar Gombe nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, inda suka yi alƙawarin fafatawa ba tare da tashin hankali ba, sabani ba tare da ƙiyayya ba, tare da amfani da fasahar zamani wajen wayar da kan jama’a maimakon tunzura su.

Labarai

Post navigation

Previous Post: INEC Ta Ce Ta Kammala Shirye-Shiryen Zaɓen Cike Gurbi A Gombe
Next Post: Maryam Dan’azumi Ta Zama Abin Alfahari Ga Najeriya Bayan Lashe Gasar Alƙur’ani Ta Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Venezuela Ta Sako Karin Mutanen Da Take Tsare Dasu Labarai
NANPAN Ta Wayar Da Al’umma Kan Amfanin Shayar Da Jarirai Nono Kaɗai Afrika
Hukumar Zabe Ta Saukaka Gudanar Da Rijistar Katin Zabe A Najeriya Labarai
Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC Afrika
SERVICOM, ATBUTH Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Labarai
Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Maryam Dan’azumi Ta Zama Abin Alfahari Ga Najeriya Bayan Lashe Gasar Alƙur’ani Ta Duniya
  • Gabanin Zaɓe: Jam’iyyun Siyasa Sun Ƙuduri Aniyar Kare Zaman Lafiyar Jihar Gombe
  • INEC Ta Ce Ta Kammala Shirye-Shiryen Zaɓen Cike Gurbi A Gombe
  • Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini
  • Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hamas Ta Mika Ma Isra’ila Gawar Daya Daga Cikin Mutane Biyu Sauran Duniya
  • Sabuwar Shekarar Musulunci 1448: Kiristoci Sun Yi Murna, Sunyi Kiran Samar Da Hutu Ga Shekarar Musulunci Afrika
  • Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai
  • Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja Afrika
  • Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai
  • Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
  • Baba Malam Ya Lallasa Abokan Hamayya Da Kuri’u Sama Da Dubu 236 A Zaben Fidda Gwani Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.