Ghana ta haramta hakar ma’adnai a gandunan dajin kasar data kebe, a wani mataki na kare muhhalli, da suka hada da ruwa, da kuma kare share da dazuka a kasar, kamar yadda ma’aikatar kare muhalli, kimiyya da fasaha ta sanar.
Ghana wacce take kan gaba wajen hakar zinai, tana fuskantar hauhawar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wadda hakan yake lalata gonakin noman cocoa, da suke lalata dazuka da kogunan, da suke barazana ga sashen hakar ma’adinai a ksar.
Mannyan kamfanonin hakar ma’adnai suna bada rahotannin kkutse daga kananan mahaka ba bisa ka’ida, lamari da ya tilastawa kamfanonin su kara daukan matakan tsaro, da suka hada da jiragen dornes, da daukan msu gadi.
Yanzu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, ya bazuu zuwa kashi 13 cikin sassan ksar 16 da ake hakar ma’adinai, da suka hada da sassan da suka yi suna wajen noman cocoa a gabashi da kuma yammacin kasar, kamaar yadda alkaluman huuma suk nuna. Gwammnatin kasar tana garambawul ga sashen hakar ma’adinai da wajen bada lasisi, da kuma karafafa tsaro da nufin shawo kan matsalar rashiin bin ka’ida.
Ahllinda ake ciki kuma, masana sunce akwai alammun darajar kudaden Ghana da Zambia za su fadi a fagen canji a makon gobe, yayinda babu wani canji da ake gani a canjin kudaden Najeriya, da Kenya da Uganda, a canji da dalar Amurka.


