Tinubu ya kafa kwamitin sasanci da dabaru domin karfafa APC gabanin zaben 2027.
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani kwamitin dabaru, sasanta rikice-rikice da wayar da kai domin magance sabanin cikin jam’iyyar APC yayin da ake tunkarar zaben 2027, An kaddamar da kwamitin ne a ranar Laraba a Lagos.

Kwamitin ya kunshi gwamnoni, mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da manyan jiga-jigan jam’iyyar, inda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ke matsayin shugaba, yayin da Muiz Banire ke matsayin sakatare.
Da yake jawabi, Buni ya ce kwamitin zai yi aiki da gaskiya da jajircewa, tare da tabbatar da adalci da bai wa kowa damar jin yana cikin tafiyar jam’iyyar, Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar hadin kai da hakuri a cikin APC, yana mai cewa hakan ne kadai zai tabbatar da dorewar dimokuradiyya da inganta jam’iyyar.


