Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi
Published: December 11, 2025 at 10:54 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Kano za ta dauki sabbin malaman makaranta dubu hudu a fadin jihar.

Shugaban Hukumar Ilimi Matakin Farko a jihar, (SUBEB), Yusuf Kabir, ya ce hukumar na shirin daukar karin malamai dubu hudu domin karfafa koyar da karatu a Matakin farko da lissafi a kananan hukumomin jihar.

Ya bayyana hakan ne a taron bitar sakamakon karatun dalibai na ƙarshen shekarar 2025, wanda aka shirya domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ci gaban koyon ilimi a karkashin shirin Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE) na tsawon shekaru uku, wanda gwamnatin Birtaniya ke tallafawa.

Kabir, wanda sakatariyar hukumar, Hajiya Amina Umar, ta wakilta, ya bayyana cewa duk da cewa malamai 4,343 aka dauka a karin daukar ma’aikatan baya-bayan nan, amma har yanzu jihar na fama da karancin malamai.

A cikin sabbin gyare-gyaren da ake shirin aiwatarwa, jihar na kokarin rage cunkoson aji daga tsarin malami daya kan dalibai 132 a wasu ajujuwa zuwa burin samun malami daya kan dalibai 60.

Wani mai ruwa da tsaki, Dr. Miswaru Bello, ya bayyana damuwa cewa kashi 40% na daliban Kano ba sa halartar aji, yayin da rashin halartar malamai ke kaiwa kusan kashi 12%.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa
Next Post: Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano

Karin Labarai Masu Alaka

Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike a Tituna Najeriya
An Damke Wani Likita Da Ke Taimakawa ‘Yan-Ta’adda Najeriya
Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya
Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike a Tituna
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakuncin Wasannin Afirka Na 2031.
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Rediyo
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gangamin Wayar Da Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Jihar Gombe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
  • Kirana Ga ‘Yan Siyasar Arewa, Su Jira Sai 2031- Akume Labarai
  • Kama Muhyi Magaji Siyasa ce Kawai Inji Gwamnatin Kano Labarai
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Masana: ‘Yancin Kasashen Afrika A Rubuce Yake Ba A Zahirance Ba Najeriya
  • Shirin Manuniya Kashi Na Daya, Yau Juma’a 11.21.25 Shirye-Shirye
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.