Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Sokoto Tabada Umarnin Biyan Albashin Watan Feburairu
Published: February 12, 2026 at 4:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayar da umarnin a fara biyan ma’aikatan jihar albashin watan Fabarairu nan take, domin sauƙaƙa musu shirye-shiryen tunkarar watan azumin Ramadan da ke ƙaratowa.

Sanarwar hakan ta fito ne a ranar Alhamis ta hannun shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin gwamnan, Abubakar Bawa, inda ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa ma’aikata da masu karɓar fansho a wannan lokaci mai muhimmanci ga al’ummar Musulmi.

A cewar sanarwar, matakin ya shafi ma’aikatan gwamnatin jiha, da na ƙananan hukumomi, da ma’aikatan Hukumar Ilimi ta Ƙananan Hukumomi, tare da tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a faɗin jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a fara aiwatar da biyan albashin ne daga ranar Juma’a, 13 ga watan Fabarairu.

Ana sa ran al’ummar Musulmi a sassa daban-daban na duniya za su fara azumin watan Ramadan a ranar 18 ko 19 ga watan Fabarairu, gwargwadon yadda aka ga watan.

Matakin na gwamnan ya samu karɓuwa daga wasu sassa na al’umma, inda ake ganin hakan zai taimaka wa ma’aikata da masu fansho wajen gudanar da hidimomin rayuwa cikin sauƙi yayin azumi.

Labarai, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya

Karin Labarai Masu Alaka

Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
Shugaba Tinubu ya mika sunayen Sabbin Shugabannin NMDPRA da NUPRC Bayan Murabus Din Farouk Ahmad Da Gbenga Komolafe Najeriya
Dakarun Gwamnatin Kasar Sham Tayi Mamaya Zuwa Gabashin Kasar Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai
Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio) Labarai
Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gwamnatin Sokoto Tabada Umarnin Biyan Albashin Watan Feburairu
  • Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya
  • Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya
  • Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa
  • Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Yajin Aikin Ma’aikatan Lafiya Na Shafar Harkokin Jinya A Asibitoci Kiwon Lafiya
  • Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
  • Gwamna Ododo Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya Najeriya
  • Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato Tsaro
  • Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutu Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.