Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ba Mu Goyon Bayan Kowane Dan Takara A 2027 – ASUU Afrika
  • Wakilai Daga Ƙasashen Duniya Za Su Halarci Taron Hulɗa Da Jama’a A Abuja Afrika
  • Pasto Buru Ya Karrama Malamin JNI Kan Ƙoƙarin Samar Da Zaman Lafiya A Arewacin Najeriya Afrika
  • An Kashe Shugaban Fulani Makiyaya A Najeriya Afrika
  • Afirka Na Bukatar Adalci Da Tallafin Kuɗi Wajen Yaƙi Da Sauyin Yanayi – ACR Afrika

Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya
Published: February 12, 2026 at 8:47 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

An gudanar da sallar roƙon ruwa a Saudiyya saboda ƙarancin ruwa da tsananin zafi dake kasar take Fuskanta.

A safiyar yau, Alhamis, an gudanar da sallar roƙon ruwa (Salat al-Istisqa) a wurare daban-daban a faɗin ƙasar Saudiyya, bisa umarnin hukumomin addini da gwamnati, domin neman rahamar Allah bayan dogon lokaci ba tare da samun ruwan sama ba.

Dubban jama’a sun halarci sallar a masallatai da filayen idi a manyan birane kamar Riyadh, Makkah, Madinah, da Dammam, inda aka yi addu’o’i na musamman domin Allah Ya sauƙar da albarkar ruwan sama, Ya kuma dawo da nutsuwa ga ƙasa da mazaunanta.

Rahotanni sun nuna cewa ƙasar na fuskantar matsalar tsananin zafi da ƙarancin ruwa, wanda ya shafi amfanin gona da rayuwar jama’a. Hukumomi sun buƙaci al’umma da su ci gaba da yin istigfari da roƙon gafarar Allah, tare da yin addu’a domin samun sauƙi da rahamarsa

A cewar malamai, irin wannan salla na daga cikin hanyoyin da Manzon Allah (SAW) ya koyar domin neman taimakon Allah lokacin fari ko matsalar yanayi.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa
Next Post: Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika
Kwararru Sun Tabbatar Da Lafiyar Kangimi Dam Bayan Binciken Tsaro Afrika
Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
“Hotuna” An Sako Daliban Makarantar St. Mary’s Su 100 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
Sojojin Amurka Sun Kutsa Cikin Kasar Iran Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ba Mu Goyon Bayan Kowane Dan Takara A 2027 – ASUU
  • Jami’in NSCDC Ya Harbe Direban Tirela A Gombe
  • Wakilai Daga Ƙasashen Duniya Za Su Halarci Taron Hulɗa Da Jama’a A Abuja
  • Pasto Buru Ya Karrama Malamin JNI Kan Ƙoƙarin Samar Da Zaman Lafiya A Arewacin Najeriya
  • An Kashe Shugaban Fulani Makiyaya A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sanda A Jihar Katsina Najeriya
  • ECOWAS Ta Saka Dokar Ta Baci A Afrika Ta Yamma Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
  • Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
  • Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
  • Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
  • Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai
  • Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.