Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida A Mulkin Tinubu
Published: December 3, 2025 at 5:53 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 3, 2025

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida, kare dimokiraɗiyya, da tabbatar da tsaro a fagen yaɗa labarai a Najeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a Taron Shekara-shekara na Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI) da aka gudanar a ranar Talata a otal ɗin NICON Luxury da ke Abuja.

Idris ya bayyana kafofin watsa labarai a matsayin “hanyar sadarwa mafi muhimmanci ta kowace dimokiraɗiyya, kuma mai ƙara ƙarfafa muryar ’yan ƙasa.”

Ya ce halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wajen buɗe taron ya nuna yadda gwamnati take buɗe ƙofa ga tattaunawa da manema labarai.

Da yake magana kan taken taron, wato “Magance Musguna Wa Kafofin Watsa Labarai a Nijeriya,” Ministan ya ce dole ne a bambanta abubuwan da suka faru a baya da kuma yanayin da ake ciki a yau.

Ya bayyana cewa, “Babu wata manufa ta gwamnati da ke neman takura kafofin watsa labarai a yau,” yana mai cewa hujjoji suna nuna kamewa da haɗin kai, ba ƙiyayya ba.

Ya ce: “Tattaunawa kan ’yanci dole ta ta’allaƙa ne a kan gaskiya. Idan wani ya yi iƙirarin cewa akwai wata manufa ta musgunawa a yau, ya kamata mu auna wannan iƙirari da hujjoji.”

Idris ya ce hukumomin tsaro yanzu suna aiki ne ƙarƙashin ƙa’idoji masu tsauri domin tabbatar da amincin ’yan jarida, musamman a lokutan zanga-zanga ko wuraren da ake ganin rikice-rikice.

Ya kuma bayyana cewa hukumomin da ke kula da yadda kafafen yaɗa labarai ke aiki suna ci gaba da samar da muhallin da ya dace, mai tsari da gaskiya.

Ya ce: “’Yantar da kafofin watsa labarai abu ne da ba za a iya watsar da shi ba. Dole ne ’yan jarida su iya yin aikin su ba tare da tsoratarwa ko tsoma baki ba, kuma wannan gwamnati ta kasance a ko da yaushe a kan wannan matsayi.”

Ya kuma ambaci wani rahoto da wata jarida ta wallafa rahoto mara kyau da ya yi iƙirarin cewa wai Nijeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ke tilasta karɓar haƙƙin ‘yan luwaɗi da maɗigo.

Ya ce duk da cewa rahoton na iya tayar da rikicin addini da al’ada, gwamnati ta zaɓi gaskiya maimakon husuma.

Idris ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta buga cikakken rubutun yarjejeniyar, ta fitar da bayanai na gaskiya, ta tattauna da jama’a a fili, sannan ta kai ƙorafi ta hanyar mai duba aikin jaridu mai zaman kan sa. Ba mu yi amfani da matsin lamba ko tilastawa ba. Mun zaɓi gaskiya.”

Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya za ta karɓi baƙuncin Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai (IMIL) na Afrika, wadda za ta riƙa horar da ’yan jarida, malamai, da al’umma kan yadda ake yin aikin jarida cikin gaskiya, tantance bayanai, da yaƙi da yaɗa ƙarya bisa tsarin al’adu na Afrika.

Ya ce cibiyar za ta kasance mai zaman kan ta, wadda ke dogaro da ilimi ba tare da zama mai magana da yawun gwamnati ba.

Ya ce za a ƙaddamar da ita a farkon watannin 2026.

Haka kuma, Idris ya tabbatar da shirye-shiryen gwamnati na yin aiki tare da IPI reshen Nijeriya, Ƙungiyar Editocin Nijeriya, da Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya domin sabunta tsarin dokokin kafafen yaɗa labarai bisa ƙa’idojin duniya, tare da kiyaye ’yancin magana da muradun jama’a.

Ya ce: “Haƙƙin mu mu duka ba wai kawai ƙalubalantar musgunawa ba ne, har ma da faɗaɗa ‘yanci. Mu ƙarfafa ginshiƙan dimokiraɗiyyar mu ta hanyar kare ‘yancin da ke tabbatar da dorewar ta.”

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda shi ne ya jagoranci buɗe taron.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Majalisar Dattawa Ta Wanke Janar Christopher Musa A Matsayin Minista
Next Post: Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgin Sojin Saman Najeriya Yayi Hatsari a Jihar Neja Labarai
Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin Labarai
Kirana Ga ‘Yan Siyasar Arewa, Su Jira Sai 2031- Akume Labarai
Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai
Tsananta Hukunci Ga Masu Fyade Kan Takaita Cin Zarafin Yara Labarai
Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike a Tituna
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakuncin Wasannin Afirka Na 2031.
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Rediyo
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari Labarai
  • Gwamnatin Jihar Kano Zata Kashe Makudan Kudade Ga Jama’ar Kano! Najeriya
  • Masana: ‘Yancin Kasashen Afrika A Rubuce Yake Ba A Zahirance Ba Najeriya
  • Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara Wasanni
  • Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya
  • Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
  • Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba” Wasanni
  • Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.