Indonesia tace kudurin kafa rundunar kiyaye zaman lafiya a Gaza, zai bukaci sojoji dubu ashirin, hukumomi a Jakarta suna ganin kasar zata bada dakaru dubu takwas cikin wannan adadi, kamar yadda kakakin shugaban kasar Prabowo Subianto ya fada ranar talata.
Sai dai kakakin yace ba’a bayyana sharudda tura sojojin da kuma bangaren da za su yi aiki ba.
An gayyaci shugaba Prabowo zuwa Washington cikin watan nan domin taron farko na kwamitin zaman lafiya da shugaba Donald Trump ya kafa. Indonesia wacce take a kudu maso gabashin Asiya, bara tace a shirye take wajen tura sojojinta har dubu 20, domin aikin kiyaye zaman lafiya, sai dai tace tana dakon bayanai kan aikin da za su yi kamin ta turasu gabas ta tsakiya.


