Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Karɓi Baƙuncin Jakadan Ƙasar China, Yu Dunhai
A ranar Juma’a, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi Jakadan China a Najeriya Mr. Yu Dunhai tare da wani jami’in ofishin jakadancin, Mr. Zhu Songbo, a fadar shugaban ƙasa.
Ziyarar ta nuna ci gaba da dangantaka mai ƙarfi tsakanin Najeriya da China musamman a fannonin tattalin arziki, zuba jari, da alaka a
tsakanin ƙasashen biyu.


