Masu sauraron GTA Hausa Amurka ke Magana barkanmu da dawowa sabon shirin GA FILI GA DOKI da ke kawo muhawara tsakanin sassa biyu masu bambancin ra’ayi ko matsaya don tabbatar da gaskiya.
Duk mako sai wani sabon lamari ya fito da ya shafi babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP da kuma babban zaben Najeriya da za a yi in Allah ya kai mu 2027.
Dambarwar shugabancin PDP ta so zuwa karshe bayan babban taron jam’iyyar a Badun da ya fito da Barista Tanimu Turaki a matsayin shugaba amma ya na fama da tarnakin kara a kotu na hurumin zaben.
A wata alama ta neman kwatar kai ba don dambarwar jam’iyya ba, gwamnan Ribas Siminalayi Fubara ya yi wa fadar Aso Rock tsinke inda bayan ganawa da shugaba Tinubu sai ya garzaya Fatakwal ya ayyana ficewa daga PDP ya koma APC.
Ba mamaki don da kyar ya kwaci kan sa daga kahon zuka na ministan Abuja Nyesom Wike da dokar ta baci da ta kawar da shi na tsawon wata 6.
Fubara ya ce ya yi hakan ne don samun damar marawa shugaba Tinubu baya. Gwamnonin PDP na ta tsukewa kamar tafkin Chadi.


