Wani jirgin yaki mai suna Alpha Jet na Rundunar Sojin Saman Najeriya ya yi hatsari a kusa da Karabonde, karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja, a yau Asabar.
hatsarin wanda ya faru misalin ƙarfe 4:10 na yamma, inda matukan jirgin biyu suka yi nasarar ficewa kafin jirgin ya faɗi ya kama da wuta.
Jirgin, wanda ya tashi daga sansanin sojin sama na Kayinji, ya samu matsala ne yayin gwajin tashi bayan bincike, kamar yadda sanarwar Rundunar Sojin Sama ta bayyana.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce matukan sun karkatar da jirgin daga yankunan da ake da cunkoso kafin su sauka da Jirgin cikin aminci.
Rundunar ta yaba jarumtaka da ƙwarewar matukan da suka ceci rayukan su, da kuma karkatar da hadarin daga wurin da al’umma suke.


