Shugaban kula da hakar ma’adanai na Jamhuriyar Demokradiyar Congo ya ce kasar sa ta dau alwashin ci gaba da tsarin rarraba ma’adanin cobalt da ake ba masu hakan ma’adanai a shekarar 2025 duk da tsaikon da aka samu na watanni karkashin sabbin dokokin, a yayin da ake shirye shiryen fara fitar da ma’adanin nan da ‘yan kwanaki.
Kasar, wadda ita ce ke samar da ma’adanin cobalt da yafi kowanne yawa a duniya , kimanin kashi 70 cikin dari, ta gabatar da tsarin rabon a watan Oktoba bayan kafa dokar hana fitar da ma’adanin da ta yi watanni da dama tana aiki, saboda kada ya zama ruwan dare, da kuma samun daidaiton farashi, amma kuma fitar da ma’adanin ta tsaya cak yayin da kamfanonin ke jiran tabbacin abin da ya kamata su yi.
A wasikar da ta aikewa ma’aikatar ma’adanai, hukumar ma’adanai ta Congo ta bukaci tattaunawa da hukumar AERCOMS me tsara hakar ma’adanai, kan tsaikon da ake samu da kuma kayan da aka kayyade mata na kashi 10 cikin dari, amma har yanzu bata ji daga gare su ba.


