Kasar Iran ta yi barazanar kai hare-haren ramuwar gayya a kan Isra’ila wadda ta yi luguden wuta babu kaukautawa jiya laraba a kan Lebanon, in da ta kashe daruruwan mutane.
Iran ta ce a irin wannan yanayi, babu wata fa’ida ta yin tattanawar kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin da Amurka.
Wannan kashedin da ya fito ta bakin jagoran masu shawara na kasar Iran, wato kakakin majalisar dokoki Mohammed Bager Qalibaf, ya nuna zaman rashin sanin tabbas da ake ci gaba da shi a yankin a bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana a ranar talata.
Bangarorin biyu sun bayyana manufofin kishiyoyin juna game da shawarwarin neman zaman lafiyar da ake shirin farawa ranar asabar. Ba a ma san ko tsagaita wutar zata dore har zuwa lokacin da za a fara tattaunawar ba.
Qalibaf ya ce tuni kasar bani Ira’ila ta karya wasu daga cikin ka’idojin tsagaita wutar ta hanyar zafafa hare-hare a kan ‘yan Hezbollah masu goyon bayan Iran a Lebanon, a yayin da ita ma Amurka ta keta ka’idojin ta hanyar nacewa a kan lallai Iran ta yi watsi da shirinta na nukiliya.
Ya fada cikin wata sanarwa cewa a irin wannan yanayi, babu wata fa’ida ga tsagaita wuta ko yin shawarwari.
Amurka da Isra’ila sun ce wannan tsagaita wuta ba ta shafi abubuwan da suke faruwa a Lebanon ba, har ma firayim minista Benjamin Netanyahu yayi alwashin ci gaba da kai hare-hare.
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, wanda zai jagoranci tawagar mashawartan Amurka ya fadawa ‘yan jarida a Budapest cewa yana tsammanin (ran ta zaci cewa tsagaita wutar ta hada har da Lebanon ne, amma abin ba haka yake ba.
Duk da yake kowace daya daga cikin Amurka da Iran ta yi ikirarin samun nasara a yakin da aka gwabza na makonni 5, har yanzu ba a warware ko daya daga cikin muhimman batutuwan da suka takaddamar a kai ba. Kowaccensu ta dage a kan cimma muradunta a yarjejeniyar da zata shata alkiblar yanayin gabas ta tsakiya na shekaru masu yawa.
Hukumar tsaron fararen hula ta Lebanon ta ce Isra’ila ta kashe mutane 254 a hare-haren da ta kai cikin kasar jiya laraba. An kashe mafi yawa a Beirut babban birnin kasar inda mutane 91 suka mutu.
Ita ma Iran an ce ta kai hare-hare kan cibiyoyin mai a kasashen yankin Gulf, ciki har da wani bututun mai na Saudiyya da ake amfani da shi wajen kaucewa mashigin ruwan Hormuz da Iran ta garkame. Kuwait da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa duk sun bada rahotannin hare-haren makamai masu linzami da jiragen drone.
Har yanzu mashigin ruwan na Hormuz yana rufe ga jiragen ruwan da ba su karbi takardar izinin shigewa ba. Masu safarar jiragen ruwa sun ce su na bukatar samun cikakken bayani kafin su fara zirga zirga. Wasu alkaluman zirga zirgar jiragen ruwa sun nuna cewa jiragen ruwa biyu dauke da tutar Girka da wasu biyu dauke da tutar kasar China sun shige ta mashigin ruwan daga safiyar laraba zuwa yanzu.
A wasu sakonnin da yayi ta rubutawa a kafar sada zumunci, shugaba Trump ya ayyana kafa sabon harajin fito na kashi 50 cikin 100 kan kayayyakin duk wata kasar da ta taimaka ma Iran da makamai, koda yake doka ba ta ba shi ikon yin hakan ba.
Dubban jama’a sun fantsama kan titunan kasar Iran cikin dare suna murna dauke da tutocin kasar, yayin da suke kona tutocin Amurka da Isra’ila.
Sai dai kuma wasu daga cikinsu sun bayyana shakkun ko tsagaita wutar zata dore, wasu na cewa zai yi wuya kasar Isra’ila ta kyale a cimma wani abu ta hanyar diflomasiyya, kuma shugaban Amurka Trump na iya waye gari ya ce ya canja ra’ayinsa.


