Kenya ta sanya hanu kan wata yarjejeniyar samarda makamashi, tsakaninta da wata gidauniyar nahiyar Afirka da wani kamfanin India kan kudi dala miliyan dari uku da 11 don samarda tashoshin wutan lantarki guda biyu masu karfi, kamar yadda ma’aikatar kudin kasar ta fada.
Kasar dake gabashin Afirka ta koma hada hanu da kamfanoni masu zaman kansu domin samarda kayayyakin more rayuwa, ganin tulin bashi da gwamnati take dauke dashi.
Karkashin yarjejeiyar samarda tashoshin wutan lantarkin, gidauniyar da ake kira da turanci Afirka 50 mai cibiya a Morocco, wacce mallakar kasashen Afirka ce, zata hada kai da kamfanin na kasar India wajen tsarawa, da gina tashoshin, harda gudanar da su, kamar yadda ma’ikatar harkokin kudin kasar Kenyan ta fada.
Karkashin ita wannan yarjejeniyar, gidauniyar Afirka 50, da kawarta ta fuskar aikin, su zasu tafiyarda komai na tashoshin wutan lantarki na tsawon shekaru 30, kamar yadda yarjejeniyar ta cimma.


