An shirya taron kara wa juna sani na kwana daya don tunkarar wasannin Motsa jiki a Jihar Bauchi.
Ma’aikatar Matasa da Wasanni na jihar Bauchi a tarayyar Najeriya,ta shirya taron bita don kara wa juna Ilimi kan wasannin Motsa jiki na Matasa karo na hudu, da zai gudana a Jihar Bauchi.
Kwamishinan Ma’aikatar Matasa da Wasanni Hon Babayo Adamu Gabarin, wadda ya samu wakilcin mai rikon Babban Sakatare a ma’aikatar Alh Abdullahi Ibrahim ya bayyana maka sudin shiya wannan taron.

Ya ce an shirya bitanne wa Jagororin Wasanni (Sport Officer) da suke kananan hukumomi ashirin dake fadin jihar Bauchi don sani ka’idoji da kuma yadda za’a ciyar da Bauchi gaba ta fanin wasannin.
Cikin bayanin sa Kwamishinan yace ya zamo dole su tabbatar da cewa sun debo ‘yan wasa na jiha banda dauko wasu a wajen jiha, ya kuma jadda aniyar gwamnati na basu goyan baya yakara da bayyana muhimmancin shirya wannan gasa shine don a samu a zakulo yara masu hazaka wa ‘yanda zasu wakilci jiha a wasannin Kasa.
Kwamishinan yace saboda maigirma Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad yayi dukkanin abunda ya dace wa bangaren Matasa da Wasanni a jiha kuma ya dukufa wajan gyara da kuma gina sabbin wajan wasanni a fadin jihar Bauchi wacce ake mata ta ke da (Mecca of Sport).

An ja hankalin mahalarta taron da su bi dokokin Gasar dan kauce wa hukunci yayin wannan wasa da za’ayi shi ranar 13 ga watan Disamba a kuma rufe 20 ga watan 10/ 2025, kwanaki bakwai kinan.
Mun samar da dukkanin kayayakin da ake bukata don ganin gasar ya tafi kamar yadda aka tsara ” in ji shi.
Kananan hukumomi ashirin ne da suke fadin jihar Bauchi zasu halarci wannan gasa inda za’ayi Wasanni kala-kala har sama da ashirin da suka shafi guje-guje tsale-tsale kokawa, to kwallon kwando, damben zamani da ma sauran wasannin irin zamani ciki harda wasannin gargaji irin su langa.
Wasannin ya kunshi bangaren Maza da Mata da ma bangaren masu bukata ta musamman wato (Para Soccer).
Manyan baki da suka halarci wannan taron sun hada da tsaffin Daraktoci a Hukumar wasanni na jihar Bauchi, da wadda ya ke kai da Shugaban Hukumar Alh Ado Amah, da wasu Jagororin gidan bangaren Mata inda dukkanin su suka bada lakca kan yadda za’a tun kari gasar cikin sauki.

Daya daga cikin mahalarta taron Abdulmalik Aminu wadda shine jami’in wasanni na karamar hukumar Bauchi, kuma Shugaban jami’ai na wasani a jiha, ya bayyana farin cikinsa da wannan taron horaswan inda yace zasuyi anfani da abunda a ka koya musu da zaran sun koma wajan aikinsu don zakulu hazikan yara da zasu fafata a gasar kuma su wakilci jiha a matakin tarayyar.

Ya kuma gode wa ma’aikatar Matasa da Wasanni na jihar Bauchi karkashin Hon Babayo Adamu Gabarin, da sukayi wannan tunani na kara wa juna sani. Yayin wannan taro an raba wa mahalarta taron takardar shaidan halartan horaswar (Certificate).


