Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tura dakarun Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tallafa wa kokarin dawo da zaman lafiya bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da amincewar a zaman majalisar ranar Talata, inda ’yan majalisa suka kada kuri’a gaba ɗaya wajen goyon bayan Kudurin.
Akpabio ya ce matakin na da muhimmanci domin rashin kwanciyar hankali a kowace kasa makwabciya na iya haifar da barazana ga yankin sannan ya ce Najeriya na da alhakin tallafawa abokan ta na Kungiyar ECOWAS.
Idan za’a iya tunawa Shugaba Tinubu ya aike da wasikar neman izini ga majalisar domin tura sojoji zuwa Kasar Benin.


