Majalissar wakilai ta rikon kwaryar jamhuriyar Nijar ta fara zamanta na biyu na karshe a shekarar nan ta 2025.
A tsawon kwanaki biyu na wannan zama wakilan zasu tattauna batutuwa da dama da suka shafi tafiyar kasar kamar yadda gwamnatin mulkin sojan kasar ta shigar da bukata. Sai dai wasu ‘yan kasar sun shawarci majalissar a kan wasu karin batutuwan da ke bukatar matakan gaggawa.
Taron Wanda ke matsayin na rufe shekarar nan ta 2025 lokaci ne da wakilai 194 na majalissar ta conseil consultatif de la refondation zasu nazarci kudirorin da gwamnatin ta Nijar ta zo da su da suka shafi fannoni da dama.
Farfesa Dicko Abdourahamane na daga cikin mahalarta taron.
Kundin tsarin mulkin gwamnatin ta rikon kwarya da ya samo asali daga babban taron rukunonin al’ummar kasar ya bai wa majalissar hurumin sauraren mimbobin gwamnati idan bukatar hakan ta taso saboda haka a wannan karon za su mori wannan dama kamar yadda shugaban kwamitin kula da siyasar duniya a majalissar CCR Bana Ibrahim ya bayyana.
Duk da cewa zaman na da mahimmanci a wajensu wasu ‘yan Nijar kamar su Salissou Ibrahim na FRSA na jan hankula a kula da wasu abubuwan da a cewarsa suna kan gaba a jerin manufofin shugaban kasa.
Shi kuma shugaban kungiyar yaki da cin hanci ta RENAC kwararre kan sha”anin shugabanci Adamou Oumarou na kokarin ankarar da zaman na wannan karon kan matakan taka birki daga yunkurin ciyo bashi daga waje.
A karshen taron na kwanaki 15 majalissar ta CCR za ta gabatar da takardun shawarwari wa bangaren zartarwa inda Janar Abdourahamane Tiani da ke da maganar karshe zai yi na’am kokuma ya bukaci majalissar ta yi Zaman gaggawa don kwaskware abinda ke bukatar gyara.


