Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta
Published: December 23, 2025 at 8:34 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rahotanni daga Afirka ta kudu suna kara bayyana yadda aka yaudari wasu ‘yan kasar suka tafi Rasha da sunan aikin tsaro ko makamancin haka, sai suka sami kansu a fagen daga a Ukraine, wani mahaifi Dubandlela yana cikin annashuwa da alfahiri lokacin da dansa dan shekaru 20 da haifuwa ya sanya hanu cikin watan Yulin bana, zai tafi Rasha inda za’a horas da jami’in tsaro da zai bada kariya ga masu hanu da shuni ko masu fada a ji.

Wata biyar bayan tafiyarsa, yanzu Dubandlela yana cike da takaici da zullumi, inda Dansa ya fada hanun mayaudara daga kungiyoyin sojojin haya, inda dansa da wasu akalla ‘yan kasar Afirka ta kudu 16 aka dauke su kuma aka tura fagen yaki a Ukraine.

Dubandlela yana aibunta kansa kan hali da dansa ya sami kansa a ciki, kuma Kakakin shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramphosa, yace gwamnati tana “daukar batun da matukar muhimmanci.”

Yace kokarin kubutar da matasan yana da sarkakiya sosai, Kuma suna magana da dukkan sassan a yakin tsakanin Rasha da Ukraine, amma Vincent Magwenya yace sun fi bada karfi ne a magana da Rasha saboda an tura matasan ne ba shiri cikin rundunar mayakanta, Ya kara da cewa sun sami labari cewa matasan suna cikin hadari sosai a yankin Donbas.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fada, yaudarar da aka yi wa matasan ba zata rasa nasaba da zargin da aka yi wa ‘yar tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, Lamari da ya tilasta mata yin murabus daga mjalaisar dokokin kasar.

Ma’aikatar harkokin wajen Rashar bata maida martani ba, da aka nemi jin ta bakinta a rubuce kan hanyoyin yaudarar matasan, da halinda suke ciki a halin yanzu

Afrika

Post navigation

Previous Post: Jami’an Tsaro: Babu Abun Tashin Hankali Kan Shawagin Jiragen Amurka
Next Post: Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran Afrika
Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta Afrika
Ana Cigaba Da Kai Kayan Agaji Kasar Morocco Sakamakon Tsananin Hunturu Afrika
Shugaban Kasar Iran Yace Kasar Bata Da Kiyayya Tsakaninta Da Amurkawa Afrika
‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
Rasuwar Tsohon Shugaban NUJ FCT, Osambedwan, Babban Rashi Ne — Ferfesa Alkali Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Umurci Janyewa Manyan Mutane ‘Yan Sanda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wikki Tourists FC: Ta Yi Sabbin ‘Yan Wasa Uku Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa Afrika
  • Ana Jimamin Mutuwar Giwa Mai Shekaru Kusan 60 A Kasar Kenya Sauran Duniya
  • Rahoton MDD Yace An Kashe Fiye Da Farar 1000 A Sudan Labarai
  • Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.