Har sai gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnonin jihohi sun yarda da cewar akwai matsaloli a bangaren tsaro a kasar, da kuma neman taimakon masana wajen magance matsalar. Idan kuwa ba a dauki wannan matakin ba, to babu shakka za’a cigaba da dulmiya rayuwar al’ummah cikin mawuyacin hali.
Tsohon Ministan Abubakar Malami, ya kara da cewar hare-haren ‘yan bindiga a kananan hukumomi da dama a jihar ta Kebbi na cigaba da ta’azzara, don kuwa kusan kullum ana dauke mutane da kashe wasu, don haka kuwa sai an tashi tsaye wajen ganin an durkufar da wadannan ‘yan ta’addan.
Talauci, rashin aikin yi, da rashin hanyoyi sun yi yawa a karkashin wannan gwamnatin, don kuwa irin yadda ‘yan tadda ke cin zarafin jama’a ko a irin lokacin kasuwancin bayi ba’a yi irin wannan cin zarafin ba, mussamman a yankin Arewacin Najeriya.


