A Najeriya kamfanin tace man fetur na Dangote, ya fada yau Litinin yana iya samarda man fetur lita bilyan daya da rabi ako wani wata. Daga nan ya gayyaci hukumomin kula da samar da man fetur a kasar su ziyarci kamfanin don su gasgata, bayanda sashen ya wallafa alkaluma da suke nuna cewa, matatar man fetur yana samar da kashi daya cikin uku na wannan adadi.
Maganganu da ake yi cewa matatun mai da suke kasar basa iya samar da wadataccen mai da Najeriya take bukata, yana daga cikin dalilan da suka sa gwamnati ta dakatar da hana shigo da tataccen mai daga ketare.
Hukumomin kasar dake sa ido sun ce Najeriya tana bukatar litan mai milyann 55 a kowace rana, ko litan mai bilyan daya da digo 67 ako wani wata.

Kamfanin yace Mai da suke samarwa a Dangote “a shirye su ke kuma suna da karfin” samarda tataccen mai lita bilyan daya da rabi a cikin watan nan na Disamba, da kuma watan Janairu, daga bisani kuma zai iya samarda litan mai bilyan daya da digo bakwai a watan Febwairu har sai yadda hali yayi.
Kamfanin matatar mai na Dangoten yace domin kaucewa duk wata kumbiya kumbiya ya gayyaci hukumomin kasar dake sa ido kan samar da man fetur su taho matatar Man daga yau daya ga watan Disamba, su wallafa alkaluman abunda matattar Man take sarrafawa ako wace rana kuma ta fadawa duniya.
Ahalinda ake ciki kuma, tattalin arzikin Najeriya ya habaka da kusan kashi hudu a cikin wata uku daga Yuli zuwa Satumba, a bangarorin da basu shafi Mai ba.


