Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya
Published: October 19, 2025 at 3:04 AM | By: Newsdesk | Updated: November 15, 2025

Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta ce ta kwato kimanin Naira biliyan 40 daga barayin biro a tsakanin jami’an gwamnati cikin shekarar nan ta 2024 mai karewa.

Shugaban IICPC Dokta Musa Adamu Aliyu ya baiyana haka a taron bitar aiyukan hukumar na shekara da ya samu halartar shugaban EFCC da sauran jagororin hukumomin da su ka shafi mu’amala da kudi.

Dr.Musa Adamu ya ce binciken da su ka gudanar ya bankado aiyukan rashawa masu ban mamaki daga bangarorin da ba a ma tsammani.

Cikin misalan da ya bayar har da karbar makudan kudi wajen biyan ma’aikatan bogi da wasu hanyoyin karkatar da kudin gwamnati.

Shugaban hukumarEFCC Ola Olukoyede ya karfafa muhimmancin aiki tare tsakanin hukumomin biyu na yaki da rashawa na Najeriya “duk aikin da ya shafi ICPC kar a kai wa EFCC hakanan duk aikin da ya shafi EFCC kar a kawo ICPC” Inji Olukoyede.

Shi kuma kwamishinan yaki da cin hanci na Saliyo da ya zama babban bako  mai jawabi ya koka kan yanda ya ce a kan gudanar da bincike mai kyau amma a kotuna sai a samu cikas wajen wa imma yanke hukunci marar tsauri ko ma masu laifi su zama an wanke su.

Daya daga mahalarta taron Dokta Sule Yau Sule ya ce matukar an yaki cin hanci to duk ‘yan kasa za su amfana da arzikin kasa.

Taron ya karfafa cewa kudaden da a ke sacewa sun kai matsayin da za su iya samar da ababen more rayuwa ga dukkan ‘yan kasa.

Labarai, Najeriya Tags:Anti Corruption, ICPC

Post navigation

Previous Post: Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata
Next Post: Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84%

Karin Labarai Masu Alaka

Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi Najeriya
Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya Labarai
Gwannatin Jihar Kebbi Ta Arawa Maniyyata Kuɗin Aikin Hajji 2026, Labarai
Amurka Zata Saidawa Saudiyya Da Jirgin Yaki Samfurin F35 Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kungiyar ECOWAS Ta Koka Game Da Yawan Juyin Mulki A Kasashen Afirka Afrika
  • Ga Fili Ga Doki Najeriya
  • Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi Afrika
  • Tabbas Za’a Gudanar Da Gasar Firimiya Lig Ta Najeriya Wasanni
  • Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11 Najeriya
  • Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
  • Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.