Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka

Oliseh, Ya Ba Eric Chelle, Shawara Da Ya Zamo Mai Tsauri AFCON 2025.
Published: December 5, 2025 at 7:33 PM | By: Bala Hassan

Tsohon kocin Super Eagles kuma kyaftin Sunday Oliseh ya ba Eric Chelle shawara mai muhimmanci.

Tsohon dan wasan Super Eagles Sunday Oliseh ya bukaci Eric Chelle da ya zamo mai tsauri da kuma kin amincewa da sa baki wajen yanke shawara kan fidda sunayen ‘yan Wasa na AFCON.

Duk da fargabar da Oliseh ke da ita game da nadin Chelle, domin ya fi son a bai wa dan Najeriya aikin maimakon wani dan Afirka, zakaran AFCON na 1994 ya yaba da kokarin da Chelle, ya yi zuwa yanzu.

Oliseh ya bayyana kwarin gwiwarsa, yana mai imanin cewa Super Eagles za su iya kaiwa dukkanin mataki a gasar cin kofin kasashen Afirka da za’ayi a Morocco.

Duk da haka, tsohon dan wasan tsakiya na Ajax ya dage cewa Chelle dole ne ya kasance mai dogewa akan abunda ya sani.

“Na san halin mutane , ina da kwarin gwiwa cewa Super Eagles za su iya yin abin da ya dace a wannan gasar,” in ji Oliseh.

“Abu na farko da nake ganin ya kamata manaja ya yi shi ne ya ɗan yi tsauri. Dole ne ya zama mai taurin kai domin ba wani abune a boye ba  cewa mutane daga waje za su yi ƙoƙarin sanya bakin su kan wanda zaiyi wasa da wanda ba zaiyi ba.

“Ina ganin dole ya tsaya tsayin daka don nuna halinsa. Shi ne ke da alhakin ƙungiyar da kuma yanke shawara kan wanda zai yi wasa.”

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Jakadan Kasar Sin a Najeriya Ya Ziyarci Tinubu
Next Post: FIFA, Ta Raba Jaddawalin Rukuni Na Gasar Kofin Duniya 2026.

Karin Labarai Masu Alaka

An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot. Wasanni
Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon Wasanni
Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu Wasanni
Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakoncin Wasannin Afirka Na 2031 Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga
  • Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030
  • ‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya
  • Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kocin Ranchers Bees Ya Yi Murabus Wasanni
  • Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Yayin Rikici A Uganda Siyasa
  • Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya
  • Shirin Manuniya Yau Juma’a 12.12.2026 Shirye-Shirye
  • Wakilan Rasha Da Ukraine Sun Tattauna A Abu Dhabi Ranar Juma’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A Nan Amurka Amurka
  • Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.