Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya gargadi cewa dole ne a kare tsarin dimokraɗiyyar Najeriya, kasancewarta kasa daya tilo da take aiwatar da demokraɗiyya a duk yankin Sahel, inda rikice rikicen siyasa da juyin mulki suka yi kamari.
Ribadu ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wani taron tattaunawa kan rigakafi wanda Kwamitin Zaman Lafiyar Kasar, Cibiyar Kukah da Ofishin Mai bawa shugaban kasa shawara ta bangaren tsaro suka shirya.
Wannan gargadi nasa ya zo ne a daidai lokacin da juyin mulki ya yi katutu a kasashen yammacin Afirka da Sahel, kamar su Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, inda aka sami hambarar da gwamnatoci.
Ribadu ya ce duk da kalubalen tsaro da na tattalin arziki da Najeriya ke fama da su, ita ce kadai kasa a yankin da har yanzu ke gudanar da mulkin farar hula bisa kundin tsarin mulki.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta samu hukuncin laifi 775 a kan masu aikata ta’addanci abin da ya ce alama ce ta ci gaban da ake samu sakamakon hadin kan hukumomin tsaro, al’umma da kuma bangaren shari’a.
Sai dai ya jaddada cewa wadannan nasarori na iya rushewa idan rikici, tashin hankali da rabuwar kai suka ci gaba da yawaita.
Ribadu ya kara da cewa ana iya samun zaman lafiya mai dorewa ne kawai idan tattaunawa ta rikide zuwa matakai na zahiri da za su kara karfin garkuwar al’umma, su dawo da amana, su kuma inganta tsaro a arewacin Najeriya.
Ya bayyana cewa yawancin matsalolin tsaro a kasa sukan fara ne daga matakin ƙananan hukumomi, yana mai jaddada muhimmancin rawar da al’umma, sarakunan gargajiya, malamai da gwamnatocin jihohi ke takawa wajen dakile rikici ya jadda da cewa idan aka bai wa al’umma damar magance matsalolinsu da kansu, buƙatar tura dakarun soja tana raguwa ƙwarai.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Bishop Matthew Kukah, ya ce matsalar tsaro ta taba kusan kowane dan Najeriya kai tsaye.
Bishop Kukah ya yi watsi da ra’ayin cewa al’umma su dauki makamai domin kare kansu, yana mai cewa daukar makami ba ya kawo tsaro na gaskiya, illa zai haifar da sabbin matsaloli a kasar.


