Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika

Ribadu: Najeriya Ce Kasa Daya Tilo Da Ke Tabbatar Da Demokraɗiyya A Sahel
Published: December 4, 2025 at 8:58 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya gargadi cewa dole ne a kare tsarin dimokraɗiyyar Najeriya, kasancewarta kasa daya tilo da take aiwatar da demokraɗiyya a duk yankin Sahel, inda rikice rikicen siyasa da juyin mulki suka yi kamari.

Ribadu ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wani taron tattaunawa kan rigakafi wanda Kwamitin Zaman Lafiyar Kasar, Cibiyar Kukah da Ofishin Mai bawa shugaban kasa shawara ta bangaren tsaro suka shirya.

Wannan gargadi nasa ya zo ne a daidai lokacin da juyin mulki ya yi katutu a kasashen yammacin Afirka da Sahel, kamar su Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, inda aka sami hambarar da gwamnatoci.

Ribadu ya ce duk da kalubalen tsaro da na tattalin arziki da Najeriya ke fama da su, ita ce kadai kasa a yankin da har yanzu ke gudanar da mulkin farar hula bisa kundin tsarin mulki.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta samu hukuncin laifi 775 a kan masu aikata ta’addanci abin da ya ce alama ce ta ci gaban da ake samu sakamakon hadin kan hukumomin tsaro, al’umma da kuma bangaren shari’a.

Sai dai ya jaddada cewa wadannan nasarori na iya rushewa idan rikici, tashin hankali da rabuwar kai suka ci gaba da yawaita.

Ribadu ya kara da cewa ana iya samun zaman lafiya mai dorewa ne kawai idan tattaunawa ta rikide zuwa matakai na zahiri da za su kara karfin garkuwar al’umma, su dawo da amana, su kuma inganta tsaro a arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa yawancin matsalolin tsaro a kasa sukan fara ne daga matakin ƙananan hukumomi, yana mai jaddada muhimmancin rawar da al’umma, sarakunan gargajiya, malamai da gwamnatocin jihohi ke takawa wajen dakile rikici ya jadda da cewa idan aka bai wa al’umma damar magance matsalolinsu da kansu, buƙatar tura dakarun soja tana raguwa ƙwarai.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Bishop Matthew Kukah, ya ce matsalar tsaro ta taba kusan kowane dan Najeriya kai tsaye.

Bishop Kukah ya yi watsi da ra’ayin cewa al’umma su dauki makamai domin kare kansu, yana mai cewa daukar makami ba ya kawo tsaro na gaskiya, illa zai haifar da sabbin matsaloli a kasar.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro
Next Post: Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya.

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti Afrika
Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin Afrika
Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Fasalin Shirin NYSC Afrika
Sabon Babin Tsaro A Najeriya: Gombe Ta Fito Da Tsarin Smart Security Na Farko Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi Afrika
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
  • Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya Najeriya
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
  • Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.