Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti
Published: June 26, 2026 at 9:28 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta bayyana cewa ta lalata gonakin wiwi masu fadin sama da hekta 51 tare da kama mutane 281 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, sayarwa da kuma amfani da su a jihar Ekiti cikin shekara guda.

Kwamandan NDLEA na jihar, Rufus Aina, ne ya bayyana hakan a Ado Ekiti yayin bikin Ranar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Duniya ta 2026.

Ya ce hukumar ta samu nasarar gurfanar da mutane 50 da aka yanke musu hukunci, yayin da sauran shari’o’i ke gaban Kotun Tarayya da ke Ado Ekiti.

Aina ya ce noman wiwi a sassa daban-daban na jihar na ci gaba da zama babban kalubale, yana mai gargadin cewa safara da amfani da miyagun kwayoyi na haddasa aikata laifuka, rashin tsaro, barin makaranta da kuma lalata rayuwar al’umma.

Ya kara da cewa cikin shekara guda da ta gabata, hukumar ta gudanar da gangamin wayar da kai 76 da shirye-shiryen rediyo da talabijin 15, tare da ba mutane 87 masu amfani da miyagun kwayoyi shawara da jinya.

Har ila yau, ya bayyana cewa an kwato miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 6,337.517, yayin da wani mutum mai suna Osho Akindele ya samu daurin shekaru 20 a gidan yari saboda laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa an kama wasu tsofaffi biyu masu shekaru 78 da 80 bisa zargin mallaka da safarar miyagun kwayoyi, yana kira ga al’umma da su hada kai da hukumomi wajen yaki da matsalar miyagun kwayoyi.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Shugaban Miyetti Allah Zai Fuskanci Shari’a Kan Zargin Badakalar Kuɗi da Ta’addanci
Next Post: Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye

Karin Labarai Masu Alaka

CNG Ta Farfado Da Jarin Masu Adaidaita Sahu A Kaduna Afrika
Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
Shugaba Tinubu Ya Shiga Takara Wa’adi Na Biyu Afrika
Isra’ila Zata Mamaye Lebanon Labarai
Fiye Da Fararen Hula 1000 Yunwa Ta Kashe A Sudan Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Najeriya Da Dubai Zasu Karbi Bakoncin Taron Zuba Hannayen Jari Najeriya
  • NEDC Ta Fara Shirin Kera Sanitary Pads A Gombe Domin Samar Da Sana’o’i Afrika
  • Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11 Najeriya
  • Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
  • Anfara Tantance Lafiyar Maniyyatan Jihar Gombe Kiwon Lafiya
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
  • An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
  • Shugaba Trump Yace Bazai Bari Iran Ta Mallaki Nukiliya Ba Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.