Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa
Published: February 12, 2026 at 8:19 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe ta ce ta samu nasarar ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a kauyen Tingile, yankin Birin Fulani da ke Karamar Hukumar Nafada a jihar Gombe Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe uku na daren ranar 11 ga Fabrairu, 2026, lokacin da wasu mutane da ba a san ko su waye ba, dauke da sanduna, adduna da wukake, suka kai hari rumfar kiwon shanun Alhaji Adamu Bappah mai shekaru 48.

Sanarwar ta ce maharan sun doke shi tare da dansa, inda dan ya samu raunuka, kafin daga bisani su yi awon gaba da Alhaji Adamu zuwa wani wuri da ba a sani ba. An garzaya da dansa asibiti domin kula da lafiyarsa.

Sai dai rundunar ta ce cikin gaggawa jami’anta, tare da hadin gwiwar mafarauta da ’yan sa-kai, suka kaddamar da samame a wannan rana da misalin karfe uku na rana. Hakan ya kai ga ceto mutumin a dajin Dawo da ke Karamar Hukumar Kwami.

Bayan ceto shi, an kai shi asibiti domin a duba lafiyarsa kafin daga bisani ya koma hannun iyalansa lafiya.

Rundunar ta kara da cewa ana ci gaba da kokarin cafke wadanda ake zargi da aikata laifin, domin su fuskanci hukunci.

’Yan sandan sun sake jaddada kudurinsu na tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar Gombe.

Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv
Next Post: Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya

Karin Labarai Masu Alaka

Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hankali Najeriya
Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya Amurka
Hukumar CAC Zata Dakatar da POS Mara Rijista a Kasar Najeriya
Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya
Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya
  • Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa
  • Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv
  • Amurka Tafara Mayar Da ‘Yan Afghanistan Da Suka Makale A Qatar
  • Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Yohanna YD Buru: Makon Haɗin Kan Addinai Ya Ƙarfafa Ilimin Zaman Lafiya A Najeriya Labarai
  • Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula Labarai
  • Tsohon Alkalin Alkalai A Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 71 Labarai
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ya Ziyarci Pindiga Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Isa Legas Domin Hutun Karshen Shekara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.