Sarkin Musulmi ya soki shugabannin addinai kan yadda ake boye gaskiya game da matsalar tsaron Najeriya
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya soki shugabannin addinai bisa rashin faɗa wa ’yan Najeriya gaskiya game da halin tsaro da ake fama da shi a ƙasar.
Yayin taron shekara-shekara na Majalisar hadin guiwa kan harkokin addinai a Najeriya (NIREC) da aka gudanar a Abuja, shugaban majalisar ya yi gargadi cewa ƙungiyar za ta zama marar amfani idan shugabanninta ba su rungumi tattaunawa ta gaskiya ba.
Maganar shugaban ta zo ne yayin da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ke matsa kaimi a dauki matakin magance rashin tsaro, a yayin da gwamnatin tarayya ke musanta zargin wariyar addini daga ƙasashen duniya.
Sarkin ya ce NIREC ta kauce daga manufarta ta asali, yana mai kira da a gyara matsalolin cikin gida da ke rage tasirin ƙungiyar.
Ya kuma nuna damuwa cewa yanayin amana da zumunci da ya saba gani a tarurruka na baya ya ragu sosai, yana mai tambayar dalilin wannan matsala.


