Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana tunanin aikewa da jirgin yaki a karo na biyu zuwa gabas ta tsakiya, duk da cewa fadar Washington da fadar gwamnatin Tehran na shirye-shiryen ci gaba da tattaunawa, kan matakan da zasu dakile aukuwar wani sabon rikici.
Kasar Oman ce ta samar da muhallin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a makon da ya gabata. Mai magana da yawun ministan harkokin wajen Iran ya ce tattaunawar zata basu damar sanin yadda fadar Washington ta dauki abun da muhimmanci, kuma yana ra’ayin ci gaba da huldar diplomasiyya.
An zauna tattaunawar ne bayan da Trump ya girke jirgin yaki daya a gabas ta tsakiya, abinda ya jawo fargabar daukan matakan soji.


